ArticleIDPicAddressSubjectDate
{ArticleID}
{Header}
{Subject}

{Comment}

 {StringDate}
 
 
 
 
 
 
 
ViewArticlePage
 
 
 
  • Fatawar mai girma Shaikhul Azhar kan halalcin aiki da Mazhbar Shi'a Ithna Ashariyya:   
  • Sendtofriend
  •  
  •  
  • Fatawar mai girma Shaikhul Azhar kan halalcin aiki da Mazhbar Shi'a Ithna Ashariyya:

    An tambaye shi cewa: "Wasu mutane suna ganin wajibi ne kan musulmi ya yi taklidi (koyi) da mazhabobin nan guda hudu sanannu, kuma babu mazhabar Shi'a Imamiyya ko Shi'a Zaidiyya a cikinsu, domin aikinsa na ibada da mu'amala ya zama ingantacce, karbabbe. Shin Malam yana muwafaka da wannan ra'ayi, misali yana hana aiki da mazhabar Shi'a Imamiyya, ga misali?"

    Sai Mai girma ya amsa da cewa:

    1. Lalle addinin Musulunci ba ya wajabtawa wani daga mabiyansa da ya bi wata mazhaba kebabbiya. Kai kowani musulmi yana da hakkin, tun daga farko, na ya bi kowace mazhaba wacce aka nakalto ta nakaltowa sahihiya wacce aka rubuta hukumce-hukumcenta cikin littattafanta kebantattu. Kuma duk wanda yake bin wata mazhaba daga wadannan mazhabobi yana da damar ya koma wata mazhabar, kowace ce kuwa. Kuma ba shi da laifi kan kome daga wannan.
    2. Lalle mazhabar Ja'afariyya wacce aka fi sani da Mazhabar Shi'a Imamiyya Ithna Ashariyya, mazhaba ce wacce ta halalta a yi ibada da ita bisa shari'a kamar sauran mazhabobin Ahlussunna. Ya kamata musulmi su san wannan, kuma su kubuta daga 'yan garanci wajen son wata mazhaba ayyananna. Addinin Allah da shari'ar-Sa (S.W.T.) ba su takaita da wata mazhaba ba. Duk (ma'abuta mazhabobin) ma'abuta ijtihadi ne karbabbu wajen Allah Ta'ala, ya halalta ga wanda bai cancanci bincike da ijtihadi ba ya yi taklidi da su da aiki da abin da suka tabbatar da shi cikin fikihunsu. Kuma babu bambanci tsakanin ibada da mu'amala a wannan".

    (Mahmud Shaltut)


    Maganar Dr. Muhammad Muhammad Fahham,
    Shehin Jami'ar Azhar dangane da fatatar Shaik Shaltut:

    "Allah Ya jikan Shaikh Shaltut wanda ya waiwaici wannan ma'ana mai girma ya dawwamar da ita cikin fatawarsa mabayyaniya mai gwarzantaka, yayin da ya yi furuci da halalcin aiki da mazhabar Shi'a Imamiyya yana mai daukar ta a matsayin mazhabar fikihu a Musulunci, mai dogara kan Littafin Allah da Sunna da dalili. Allah na ke roko Ya ba da dacewa wa masu aiki bisa wannan tafarki mai girma na gane juna cikin 'yan'uwa masu bin akidar gaskiya ta Musulunci".

    "Kuma ka ce: Ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku, da ManzonSa da kuma muminai".

    Kuma karshen kiranmu Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai".

    (Muhammad Muhammad Fahham) In an duba za a ga cewa hanyar hada kan al'umma bude take ga duk mai ikhlasi daga 'yan'uwa musulmi, wajibi ne su hada sahu guda, su jefar da sassabawa da 'yan garanci, su tuge dalilan rarraba, su gurfanar da ra'ayoyin ilmi gaban bincike da tattaunawa domin a gano gaskiya.

    Mu muna kiran al'ummar musulmi ko ina suke da su fahimci irin halin kunci da musulmi suke ciki na siyasa da zamantakewar jama'a, su kuma yi aiki kan hada kan musulmi da watsar da rarrabuwa, kuma su gano wanda yake rura wutar sabani da 'yan garanci, domin su nesance shi. Domin ya wajaba mu sani cewa muna fama da kulle-kullen Yahudawa Sahyoniya da 'yan mulkin mallaka na Gabashi da Yammaci da 'yan barandansu.

    Daga karshe, muna rokon Allah Mai Daukaka, Mai iko da Ya hada kan al'ummar musulmi, Ya nisantar da masu dasisa da masu rura wutar fitina tsakanin al'ummar musulmi da tozarta masu aikin tabbatar da shari'ar Allah da masu kira zuwa gare Shi. Domin akwai taimakawa abokan gaban Allah da hidima ga azzaluman duniya cikin raunana hadin kan musulmi da yada rarraba tsakanin rundunonin masu jihadi da kira zuwa ga Allah.

    "Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku, da ManzonSa da kuma muminai". (Surar Tauba, 9: 105).

    Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai.

    Wallafar: Mu'assasar Al-Balagh

    Fassarar: Ammar Kumo