ArticleIDPicAddressSubjectDate
{ArticleID}
{Header}
{Subject}

{Comment}

 {StringDate}
 
 
 
 
 
 
 
ViewArticlePage
 
 
 
  • Siyasar Musulunci Ko Musuluncin Siyasa?!  
  • Sendtofriend
  •  
  •  
  • Siyasar Musulunci Ko Musuluncin Siyasa?!

    Siyasar musulunci: Al'amari ne da ya shafi jagorancin jama'ar musulma kamar yadda yake bisa dokokin shari'a. Amma musuluncin siyasa abu ne maras kyau, domin shi ne amfani da wata manufa domin samun cimma wani hadafi da guri.

    Ma'anar farko wato siyasar musulunci tana da kyau domin amfani ne da siyasa domin yin hidima ga addini, amma ma'ana biyu ta munana matuka domin tana nufin a yi amfani da musulunci ne domin cimma wani buri ko hadafi na siyasa, wannan lamari matuka ya munana kuma mun ga misalansa a siyasar duniya a kasashe daban-daban. Kuma da ma'ana ta biyu ne wasu suka yi raddi ga wani shehi kan sukan da ya yi wa babban marja'in nan Ayatul-Lahi Sistani (H), suka nuna cewa sukan da ya yi wa mar'ja'in kan wasu mas'aloli yana iya komawa zuwa ga cewa; shi mai sukan ya riki musuluncin siyasa ne ba siyasar musulunci ba!.

    Idan ba a manta ba kusan shekara guda ke nan da ta wuce na fara wani bahasi da na sanya wa suna dandalin siyasa wanda mun kai DANDALIN SIYASA 10, wanda ayyuka masu yawa suka hana ni ci gaba, amma yanzu ina ganin ya kamata ya ci gaba bayan wani tsari da na yi na ganin bai wa kowane lamarin lokaci komai kankantarsa, domin kada wani aiki ya shagaltar da ni ga barin wani, da fatan Allah ya agaza mana kan wannan lamari, ya sanya shi mai amfani ga al'ummar musulmi.

    Sannan kuma mun kawo siffofin da shugaba ya kamata ya siffantu da su wanda wannan ne karshen bayani da na aiko. Sannan idan ba a manta ba a farkon kowane bayani muna kawo tambaya da take nuni ga cewa bayanin amsa ne nata, kuma a haka zamu ci gaba da wannan bahasin in Allah ya so!

    Asalin Jagoranci Na Waye? Shin A Asali Wani Yana Da Hakki Ya Kasance Shugaba Kan Wani Koda Uba Ne Da Makamancinsa? Kuma Me Ake Nufi Da Allah Ne Yake Bayar Da Jagoranci? Sannan Yaya Al'umma Ta Kauce Wa Siyasar Musulunci Shin Yana Da Asali Daga Halittar Dan Adam Ko Kuwa?

    A bisa koyarwar da na samu a binciken shari'a asalin jagoranci na Allah ne, kuma koda uba da uwa suna da iyaka daga abin da Allah ya ba su na jagoranci da shugabanci kan 'ya'yansu. Don haka asalin jagoranci na Allah ne, kuma bai ba wa kowa shi ba sai mutanen da suke ya yarda da su. Amma abin da malam bahaushe yake cewa Allah ya bayar da mulki ga wani shugaba da ya samu hawa karagar mulki koda kuwa ta hanyar bindiga ne da fashin jagoranci ko kuma ta hanyar zabe koda kuwa ingantacce ne ba ma gurbatacce ba da muke da shi a kasashenmu to wannan ba shi da ma'ana da mahanga ta kwarai. Idan dai yana nufin shi ne Allah ya wakilta a kan bayi to wannan shi ne ainihin kafirci da kirar karya ga Allah, da wannan ma'anar Allah bai taba bayar da mulki ga wani ba. Amma idan ana nufin yana cikin abin da aka rubuta zai wakana a duniyar nan to wannan haka yake, sai dai abin takaici malama bahaushe yana jingina wa Allah wannan ne da ma'anar farko sakamakon mummunar akidar nan ta tilasci da ake jingina Allah duk wata barna da ita.

    Don haka Allah bai taba sanya wa mutane shugaba mabarnaci ko wanda ba ma'asumi ba, amma yayin da aka samu sabawar mutane ga biyayya ga annabawa (a.s) da wasiyyansu to babu makawa a hukuncin lalurar samun jagora a al'umma ya zama dole su sanya jagora mumini adali kai koda kuwa bai ma san Allah ba domin tsara lamurran al'umma da ya hada da kare jinni, da dukiya, da mutunci, da tsaro, da lafiya, da adalci tsakaninsu da sauransu.

    Asalin jagoranci na Allah ne, kuma shi yake bayar da shi ga wanda ya so da ma'anar farko da muka kawo, kuma wannan yana nuni da amsar da manzon Allah (s.a.w) ya ba wa Banu Amir Bn Sa'asa'a yayin da suka shardanta musulunta a kan ya ba su jagoranci bayansa (Duba Sirar Ibn Hisham: 2; 33, da Assiratul Halbiyya: 2; 3 da sauransu).

    Al'umma ta shiga faganniya ne bayan ta sauke jagorancin da Allah (s.w.t) ya dora mata ta yi watsi da shi, hasali ma ta kashe duk wadanda Annabi (a.s) ya yi mata wasiyyar biyayya garesu daya bayan daya, don haka sai ta fada cikin faganniyar da ta fi ta shekaru arba'in din Banu Isra'ila muni wacce babu kaico kan duk abin da ya same ta na wahalhalu da rukushi.

    Wannan lamari yana karfafa ra'ayin cewa dan Adam a asalinsa shi ne ya karkata zuwa ga barna da fada wa halaka da tabewa sai dai wanda ya yi imani da aiki na gaskiya, kuma wannan imanin yana misaltuwa da bayyana a ayyuka ne da zance sakamakon abin da yake fisowa ne daga cikin zukata. Surar Al'asr tana yi mana nuni da wannan babban darasi na asalin mutum ta hanyar toge masu tsira daga mutane da cewa su ne wadanda suka yi aiki na gari kawai. Sannan akwai wata hikima da ta zo a ruwayoyin hikima da wani babban shehin malami[1]yake yawan maimaita ta yana mai cewa: "Ban yi mamakin wanda ya halaka ba yaya ya halaka, sai dai na yi mamakin wanda ya tsira ne yaya ya tsira".

    Sannan sakamakon wannan tabewar da wahalar tana koma wa ne ga dukkan mutane da daidaikunsu, Don haka akwai kuskure wasu su dauka wannan lamarin ya shafi lahira kawai banda duniya, wannan dokar Allah ta tabar da maras aiki na gari tana hawa kan mutane gaba daya kamar al'umma kuma tana hawa kan daidaiku gaba daya, sannan tana shafar lamarin lahira da na duniya ne gaba daya.

    Domin gudun kada wani ya dauka mun yi nisa da abin da muke magana don haka muke son fitar da natijar wannan rubutu kamar haka:

    Mulki na Allah ne yana ba wa wanda ya so amma ba da ma'anar da muka saba jin mutane a titian da rumfunan kasuwa suna fada ba, kai ya saba wa hatta ma'anar da muka sha jin wasu na shelanta wa a Radio.

    Kaucewa wannan tsarin jagoranci na siyasar musuluinci ya sanya al'umma dukkanta a matsayinta na dunkulalliyar al'umma da daidaikunta duka fadawa faganniyar da babu iyaka sai ranar da suka dawo kan wannan tsarin mai wasici. Sai dai ba tsarin da mutane suke shelantawa a yau da sunan kafa hukumar musulunci muke nufi ba domin shi ma jabu ne a mahangarmu, sai dai tsari ne muke nufi da Allah da manzonsa suka yi wa sitampin suka yarda da shi bisa wasiyyar manzon Allah (s.a.w) da ingantacciyar koyarwarsa.

    Asalin al'umma da dukkan daidaikun mutane suna samun rinjayar dabi'ar karkacewa daga tafarkin Allah (s.w.t), sai dai wanda ya kama hanyar gaskiya bisa yadda shari'a ta gindaya masa ne kawai zai tsira, wannan kuwa a matsayin al'umma ne ko daidaiku.

    Hafiz Muhammad

    Rajab 1430

    July 18, 2009


    [1]Sheikh Ayatul-Lahi Kurani.