Wa Ya Kamata Ya Kasance Jagoran Mutane?
Shi dai lamarin siyasar al'umma wato; jagorancinta wani abu ne da ya kamata ya kasance karkashin dabi'u na gari da 'yan'uwantaka, da kaunar juna, da mutunta juna, da son al'umma, da jin daukar nauyin yi musu hidima, da ganin kimar dan Adam,wannan kuwa lamari ne da yake cikin dukkan wani loko na rayuwar al'umma da ya hada da zamantakewa, da tattalin arziki, da dukkan janibobin rayuwa, Imam Ali (a.s) yana cewa: Mutane ‘yanuwa ne, duk wanda ‘yanuwantakarsa ba ta kasance saboda Allah ba to gabace, wannan kuwa saboda fadin Allah madaukaki: “Ma’abota a wannan rana makiyan juna ne sai dai masu tsoron Allah”. Surar Zuhuruf: 67.
Sannan kuma da ya tashi nuna alakar mutane sai yake cewa: Ka kyautata wa dan'uwanka nasiha, kyakkyawa ce ko mummuna, ka taimaka masa a kowane hali, ka karkata tare da shi duk inda ya karkata, kada ka nemi sakamako wajansa, domin wannan yana daga alamar kaskanci.
Kuma a matsayinsa na jagoran siyasar tafiyar da lamarin al'umma muna ganin yadda bai gushe ba shi ne alamin adalci mai girma, sunansa mai tsarki ya gwamu da kalmar adalci, ya kasance adili da yake debe kewa da adalci yake kuma himmantuwa da shi. Bai taba yarda da kaucewa daga tafarkin adalci ba da aiwatar da shi koda da kiftawar ido komai wahalar da sakamakon haka zai haifar, ya ki yarda koda kuwa domin ya karfafa hukumarsa ne ya kaucewa hanyar adalci da gaskiya.
Wannan lamarin kuwa ya faru ne sakamakon yadda yake ganin hukuma da jagorancin al'umma da kimar da yake ba wa dan Adam, da rashin daukar mulki ba komai ba ne a wurinsa sai hidima ga mutane, duba yadda yake ganin Hakkokin 'yan Adam da jagorancinsu; Wata rana Abdullahi dan Abbas ya shiga wajansa yana gyara takalminsa sai Abdullahi dan Abbas ya yi mamaki kamar imam Ali a matsayinsa na Amirul muminina mai mulkin wannan daula mai fadi yana gyara takalminsa, sai Imam ya tambaye shi cewa, mene ne kimar wannan takalmin a wajanku? Sai Dan Abbas ya ce: Ba shi da wata kima, sai imam Ali (A.S) ya ce: Wallahi ya fi soyuwa zuwa gareni fiye da shugabancinku, sai dai kawai domin in tsaida gaskiya ko don yakar barna da ma’abotanta. Mulki a wajansa yana nufin tsayar da gaskiya, da fada da bata da mutanensa.
Don haka muna iya gani a siyasar Imam Ali tare da ma’aikatansa da gwamnoninsa yadda ya yi taka-tsantsan kwarai fiye da yadda sauran ma’aikata da masu mukamai suke yi, bai taba sanya wani aiki a wani yanki na sashin duniyar musulunci ko ya dora shi kan wani aiki sai ya tabbatar da amincewa da addininsa, da kuma isarsa wajan tafiyar da al’amuran yau da kullum. Ba ya sa wani aiki domin sonsa, kawai yana bayar da aiki ga manyan musulmi zababbunsu, kamar Malik Ashtari, da Muhammad dan Abubakar, da Sahl dan Hanif, da Abdullahi dan Abbas, da makamantansu na daga wadanda suke da cikakkiyar masaniya kan al’amuran tafiyar da mulki. Ya cika su da guzuri na muhimman wasiku da ya yi bayanin sha’anin hukunci da siyasar tafiyar da lamurran kasa, kamar yadda ya iyakance musu ayyukansu da nauyin da yake kansu.
Sannan muna iya gani karara bai yi sake ba wurin taka wa duk wani mai barna daga gwamnoninsa burki ya yi kulawa da sanya ido matuka kan ma'aikatansa, Ya kasance yana bibbiyar ayyukan ma’aikatansa da gwamnoninsa, yana aika masu bincike a kansu domin su duba ayyukansu, idan ya ga ha’inci ko takaitawa a ayyukan dayansu sai ya kawar da shi, ya kuma saukar masa da mafi munin ukuba. Wannan wani dan misali ne kadan daga cikin dubunnan misalai na tafiyar da gwamnatin da ayyanannen halifan Annabi (s.a.w) kuma wasiyyinsa ya yi.
Kada dai mu ja da nisa, don haka muna iya fara matashiya da fadin cewa: Bayan mun riga mun sallama da cewa dole ne ya kasance mutum yana da shugaba da zai koma masa, kuma a hukunci na farko a nan zamu yi nuni da waye shugaba da Allah ya sanya wa bayi, sannan sai a nan gaba idan Allah ya ba mu tsawon rayuwa sai mu yi bayani a kan lamarin da yake faruwa. Domin abin da ya faru a duniya ba shi ne abin da Allah ya so ba a shari'arsa da sakonsa, koda kuwa ya kasance abu ne wanda ya so a halittarsa da nufin cewa; abin da suka so ne ya rubuta musu a lauhil mahfuz da iliminsa na tun azal cewa; da man haka zasu yi, kamar dai likita ne da yake rubuta wa maras lafiya abin da zai same shi saboda sanin ciwon da yake tare da shi, ko kuma masu hasashen yanayi da suke hasashen me zai wakana ko kuma ma'abota ilimin taurari.
Da farko dai sai mu ce; Allah ya halicci bayinsa da suka hada da mafi muhimmanci a cikinsu wanda shi ne mutum da ya fifita shi hatta a kan mala'iku, kuma ya sanya su yi masa sujada, sannan sai ya sanya shi halifansa kuma jagora na siyasa a bayan kasa, domin gyara ya ci gaba da wakana a duniya da abin da ya so ya gudana a kan bayinsa, sai dai wannan abin da ya so yana nufin so ne na wahayi da sakon shari'a ba son nufin ya wakana ba, so ne da ya taso tare da ba wa bayi 'yancin aiwatarwa ko hanuwa.
Wannan mutumin mai halifanci sai ya kasance Allah ne yake ayyana shi da kansa imma ta hanyar aiko masa mala'ika bayan shi mutumin ya zabi Allah kuma Allah ya yarda da shi, ko kuma ta hanyar shi halifan nasa wanda muke ce masa Manzo ko Annabi (a.s), ko wasiyyin Annabi, sai ya ayyana wanda zai maye gurbinsa ba tare da samun canji a sunnar Allah ba, don haka ne ba a taba samun wani Annabi da ya gabata ba sai da ya bar wasiyyinsa wanda zai maye gurbinsa, kuma ya shelanta wa al'ummarsa a karara, ko kuma ya sanar da wasu kebantattun mutane domin gudun kada sharri ya fada wa wasiyyin nasa. Har ta kawo kan mafi darajar bayinsa manzo Muhammad (s.a.w) da ya ayyana wasiyyansa goma sha biyu kamar yadda ya zo a littattafai. (Buhari da Muslim da Kafi da Yanabi'ul Mawadda Shafi: 446 bugun Istambul, d.s.s). Sai fiyayyen halitta ya ayyana su da gamammiyar ayyanawa ta siffa kamar kasancewarsu: Jirgin Annabi Nuhu (a.s), da Kofar gafara ta Banu Isra'il, da kasancewarsu dayan alkawura masu nauyi guda biyu wato Kur'ani da su Ahlul Baiti (a.s), da kuma kasancewarsu daga Kuraishawa, daga Kuma reshen Banu Hashim. Bai tsaya a nan ba sai kuma ya ayyana na farkonsu har aka yi masa bai'a a Ranar Gadir (Fara'idus simdaini: 1/77), kai sai da ma ya ambaci sauran ragowarsu daya bayan daya, sai al'umma ta kasance kamar yadda Banu Isra'il suka bijire su ma haka suka bijire; al'amari ne da ya bayar da labarin da ma zai faru; da fadinsa mai daraja cewa da sun shiga ramin kurege mu ma sai mun shiga. Malam gaskata da maganar manzon Allah (s.a.w) in ba haka ba ka tabe, hakika ya yi maganar bin sawun al'ummun da suka gabata taku-taku (Muhammad Bn Jarir Dabari: 229).
Da haka ne sai muka samu halin da muke ciki na dimuwar da ta fi munin ta shekaru arba'in din Banu Isra'il, dimuwar ta fi ta su muni saboda kimar abin da muke da shi, don haka sai duniya da lahira ta juya wa al'umma baya, kuma dimuwar wannan al'umma tana ci gaba har sai ta yi riko da waccan igiyar mai isarwa zuwa ga tsira, kuma jirgi mai haurarwa da tseratarwa daga tunkudar ambaliyar tekun bata da dimuwa.
Sai a ci gaba da sabani tsakanin al'umma, sai bangaren mabiya Ahlul Baiti (a.s) suka yi riko da cewa shugabanci sai da nassi daga Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w), daya bangaren da suka kaucewa tafarkinsu suka riki wasunsu kuwa suka tafi a kan cewa nassi daga Allah da manzosa ba dole ba ne, yana iya kasancewa da shawara da kullin masu fada-a-ji, da juyin mulki da kwata da karfin takobi (da bindiga a yau), kai har ma da yardar mutum daya daga musulmi a kan jagora (Aljami' Li'ahkamil Kur'an: 265-274). Amma Ahlul Baiti (a.s) da mabiyansu sun tafi a kan cewa; Jagoranci na Allah ne da yake bayar da shi ga wanda ya so, sauran mazhabobi suka mayar da lamarin jagoranci zuwa ga mutane su duba wanda ya yi musu.
Hafiz Muhammad
Rajab 1430
July 18, 2009