Shin Wani Mutum Wanda Ba Ma'asumi Ba Ne Zai Iya Warware Matsalar Al'umma?
Tambaya kan wannan lamarin ta zo ne sakamakon cewa muna iya ganin yadda dan Adam ya kasa warware matsalar rayuwarsa yayin da tururuwa da gara tun da Allah ya halicce su sun warware matsalarsu ta tattalin arziki da jagoranci da zamantakewar al'umma! A nan muna iya tambaya cewa shin wadannan kwari sun fi daraja wurin Allah fiye da dan Adam ne ko kuwa?
Muna iya fada da kakkausar murya cewa; Ba haka ba ne, sai dai shi dan Adam ne ya sanya kan sa cikin wannan kuncin da babu kaico a kansa domin da zabinsa ne ya kauce wa abin da Allah ya zaba masa, kuma ya kama faganniya a cikin duhun da babu wani abu da zai kara masa sai dimaucewa, don haka ne sai zalunci ya mamaye duniya gaba daya sakamakon canja zabin Allah da waninsa, sai dan Adam ya shiga faganniya, muna iya gani sakamkon kaucewa umarnin manzon Allah da wasiyyarsa yadda tun da ya yi wafati har yau lamarin wannan al'umma ta duniya bai daidaitu ba, sai ga shi yau kana iya ganin duk duniya babu inda zaka sanya kafa ya kasance lamarin zalunci bai kai ba, sai ya kasance ko'ina babu inda aka ajiye komai a mahallinsa!
Sannan kuma wannan duniyar da Allah ya halitta da rahamarsa don me ya sanya kuwa ba zata kasance azaba ba ga al'ummun cikinta alhalin ta kaucewa son Allah (s.w.t) da zabinsa ta bi nata son. Wani abin da mafi yawa suka jahilta shi ne; sun jahilci cewa jagorancin al'umma yana bukatar sanin kowane mutum da abin da yake bukata da mafararsa da makomarsa, wannan kuwa lamari ne da Allah ya ba wa wasu bayinsa don haka ne ma yake ayyana su a kan mutane.
Yaya kuwa ba zaka a ga karkacewa ba alhalin babu wanda yake da wadannan sharuddan sai wanda Allah ya zaba ya ayyana shi a cikin al'ummarsa! Kuma tarihi sheda ne mai haske a kan yadda duniya ta gani a fili yadda jagorancin ma'asuman bayi ya kasance, ta yadda aka rasa zalunci a duniya gaba daya, aka kawar da kabilanci da jahilci, aka kawar da fasikanci da alfahasha, aka kawar da yunwa da fatara, sai ga duk duniya tana zuwa tana rusunawa, tana shiga cikin addinin Allah gaba daya. (Suratul Nasri)
Wanna kuwa domin ma'asumin mutum ya fi tururwa da kudan zuma da gara sanin abin da al'umma da halittar Allah gaba daya take ciki kuma take bukata fiye da yadda suka san na halittunsu, kai ya san abin da yake cikin ruwa da tudu da nufin Allah, kuma ya san abin da ke sama da kasa, kai Allah yana sanar da shi duk abin da ya so da izininsa, ba wasa ne ba ne irin wannan mutum Allah ya sanya raba aljanna da wuta a hannunsa, kuma ya sanya cewa; duk wanda ya mutu bai bi shi ba ya yi mutuwar jahiliyya domin ubangijin da ya yi shi ya san me ya tsara a cikin halittarsa na daga sirrin da ba shi da iyaka.
Da wannan ne muke iya ganin cewa duk wanda ya riki mulkin al'umma ba ma'asumi ba to lallai ya shiga gonar da ba ta sa ba! Kuma ya yi karambanin da duk abin da ya faru a kansa a hannun Allah gobe shi ya ja!
To Me Ye Na Yi Idan Babu Ma'asumi? Kuma Da Jagoran Ainihi Da Mabiya Tafarkin Wasiyyar Annabi (s.a.w) Suke Biyayya Gareshi Ya Shiga Boyuwa Me Ya Bari?
Wani yana iya cewa; me zamu yi idan babu ma'asumi tun da ya kawu, kuma wasiyyansa sun kawu, koda yake na karshensu yana nan cikin buya da umarnin Allah da muka sani da bayaninsa duka ya zo mana daga manzon Allah (s.a.w)?
Idan ba a manta ba wannan tambayar tana iya hawa kan mabiya Ahlul Baiti (a.s) wadanda suke ganin lallai sai da nassi za a yi jagoranci, amma sauran mazhabobi da suke ganin jagoranci ba kayan Allah ba ne, don haka Allah ya yi halitta amma sai ya bar ta ta ci gashin kanta, ta shata wa kanta abin da ta ga dama, irin wannan ra'ayin wannan tambayar ba ta shafe shi ba. Su masu wannan ra'ayin babu abin da ya rage musu sai su yi ta zaben wanda suke so ya tafiyar da rayuwarsu, kuma masu wannan tunani sun riki jagorancin al'umma tun wafatin manzon Allah har yau, kuma sun zabi mutane daban-daban har da wanda zai bugu da giya ya yayyaga Kur'ani ya ce masa: Idan ranar lahira ka je wurin Allah ka gaya masa Walid ya yayyaga ni! Sun zabi mutumin da ya fi kowa shan jinin mutane da kisa! Sun zabi yaro da bai balaga ba ya hau kan mulki! Sun zabi wanda zai kashe waliyyan Allah ya keta alfarmarsu! Kai sun zabi wadanda suka yi wa zuriyar manzon Allah kisan kare dangi a lokuta daban-daban, amma wani abin mamaki shi ne duk wajibi ne wai a bi su!
Koda yake hatta da masu ra'ayin nassi wato mabiya mazhabin Ahlul Baiti (a.s) sun tafi a kan cewa duk da Allah da manzonsa sun ayyana wadanda za a bi sai dai wannan biyayyar ta su tana da fuska biyu:
Fuskar farko; Biyayya garesu a kan kowane hukunci wanda ya zo daga garesu na magana da zance da aiki. Amma fuka ta biyu; ita ce jagorancin al'umma, to ita wannan fuskar ta biyu suna iya zama jagororin al'umma kuma shugabanninta na zartar da lamurran gwamnati ne idan al'umma ta yarda, kai hatta da na farkon babu tilas a cikinsa, babu wanda ake tilastawa ya karbi musulunci. Amma kuma wannan ba ya iya kawar da hakkinsu na cewa su ne za a bi a jagorancin al'umma, don haka ne ma manzon Allah (s.a.w) ya kwatanta su da Ka'aba da sai dai a zo mata ba dai ita ta zo ba, don haka Ka'aba tana nan a Ka'aba ko mutane sun zo ko ba su zo ba. Suna nan a matsayin kofar gafara mutane sun nema ko ba su nema ba, suna nan a matsayin jirgin tsira mutane sun hau ko ba su hau ba. Abu guda ne babu a addini shi ne babu tilas!!
Sai ma'asumi da yake hujjar Allah a bayan kasa kuma wasiyyi na goma sha biyu ya bi sawun kakansa manzon Allah wajen ayyana wa mutane wanda zasu koma zuwa gareshi a lokacin boyuwarsa karama da sunayensu, sai dai bayan ya nisanta daga alaka da mutane sai ya ayyana siffofin mutanen da duk wanda yake da wadanna sharuddan to ya hau kan mutane su bi shi matukar wadannan siffofin ba su gushe masa ba.
Amma Tambaya A Nan Ita Ce; Shin Duk Wani Matsayi Ne Irin Wadannan Mutane Da Suka Cika Wadannan Sharudd