ArticleIDPicAddressSubjectDate
{ArticleID}
{Header}
{Subject}

{Comment}

 {StringDate}
 
 
 
 
 
 
 
ViewArticlePage
 
 
 
  • Da Aka Fi Sani Da Malamai Masana Allah Da Addininsa Imam Mahadi (a.s) Ya Ba Su Damar Tafiyarwa Ko Kuwa Wani Abu Ne Ya Ba Su Dama Ban Da Sauran Abubuwa?!  
  • Sendtofriend
  •  
  •  
  • Da Aka Fi Sani Da Malamai Masana Allah Da Addininsa Imam Mahadi (a.s) Ya Ba Su Damar Tafiyarwa Ko Kuwa Wani Abu Ne Ya Ba Su Dama Ban Da Sauran Abubuwa?!

    A nan ne aka tayar da jijiyoyin wuya kan mas'ala mai girma ta jagoranci; yayin da wasu daga malamai suka tafi a kan cewa; Imam Mahadi (a.s) a matsayinsa na jagoran al'umma da ya boyu daga ganewarta ta yadda suna iya ganinsa amma ba sa iya gane shi, ya bar wa malami mas'alar fatawa, da khumusi, da ganin wata ne, don haka duk wani mutum dole ne ya bi malami a kan wadannan abubuwan. Amma batun jagorancin al'umma wanda aka fi sani da siyasar musulunci ko kusa ba na malami ba ne, kuma bai samu wannan damar daga Imami (a.s) ba.

    A kan haka ne zamu ga sayyid Khu'i (k) yana tabbatar da wannan ra'ayi yana mai cewa: "Jagoranci ba ya tabbata ga malamai a lokacin boyuwa ta kowace hanya, domin jagorancin ya kebanta da Annabi (s.a.w) da Imamai (a.s) ne, abin da kawai za a iya tabbatar da shi da ruwaya lamurra biyu ne wadanda su ne zartar da hukunci, da kuma hujjar yin fatawa, amma ba su da hakkin tasarrufi a dukiyoyin gajiyayyu da waninsu na daga abin da ya shafi jagoranci, sai dai kawai abubuwan ra'ayin ijtihadi da suke da shugabanci a kansu amma ba da ma'anar da ake cewa ba ta jagoranci irin na imamai (a.s), sai dai da ma'anar suna da hakkin tasarrufi ko wakilta wani ya yi tasarrufi a cikin wadannan lamurran… don haka ne abin da yake iya tabbata ga malami shi ne hakkin tasarrufi ba hakkin jagoranci ba. (Attankih fi sharhi Urwatul Wuska, Al'ijtihad wattaklid, Mirza Ali Garawi Tabrizi, Kum 1410 H, bugu na Uku, shafi: 424).

    Wasu kuwa suka ce ya bar wa malami duk wata dama da yake da ita har da ta jagorantar al'umma a matsayin jagora kamar yadda aka fi sanin lamari da jagorancin malami, kuma Imam Khomain (k) ya kasance daga cikin wadanda suka shahara da wannan ra'ayin.

    Idan muka dauki ra'ayi na biyu; a nan ne zamu fada cikin tambayoyin da ba su da iyaka, tambayoyi ne da masu yawa da suka baibaye samuwar jagorancin malami a duniya musamman kasashen da suke da kafuwar irin wannan tsari a yanzu kamar haka:

    Matsayin majlisosin musulunci?, Dalilin jagorancin malamai?, Jagorancin malami dalili ne na hankalin harshen ruwayoyi?, Me ya sanya wasu annabawa ba su yi kokarin kafa hukuma ba?, Shin addini daban da siyasa?, Shin dole ne hakimus shar'i ya bi mafi sanin malami ko shi kansa ya zama mafi sanin malami?, Jagoranci kafawa ne ko zaben mutane?, Alakar jagora da gwamnatin da ke karbar umarnisa?, 'Yancin fadin ra'ayi sabanin na jagorancin malami?, Shin kafa hukuma aikin ne na Allah ko kuma bukata ce ta mutane?, Tawaye ga jagorancin malami yaya zai kasance?, Intikadi ga jagorancin malami me ye matsayinsa?, Idan babu malami da zai iya kafa hukuma shin ya hau kan adalan muminai suka kafa hukuma?, Idan mutane suka ce ba sa son hukumar malami bayan kafa ta yaya ke nan?, da sauran bahasosi da suka mamaye wannan lamari. Bahasoshi ne da aka samu amsoshinsu a zaurukan karatu, kuma takalo su yana iya kaiwa ga wahala, kuma ra'ayoyinmu sun bambanta, don haka sai na ga a bar lamarin ya kasance a boye, har zuwa ranar bukatarsa.

    Akwai kuma wasu masu biye musu; wadannan su ma sun yi kama da wadancan, tambayoyi ne kamar haka: Shin biyayyar jagoran yanzu a matsayinsa na malami hakikiyya ce ko hukukiyya? Mene ne hukuncin bai'a da zabe, shin abu guda ne ko kuwa?

    Kafa hukuma ganin dama ne ga malami ko wajibi ne? Kuma shin dole ne malami ya tafiyar da ita kai tsaye ko kuwa yana iya hakan ta hannun wasu salihai? Shin dole ne sai malami ya tsayar da dukkan dokoki ko kuwa zai iya yin wanda ya samu kawai? Shin akwai dokokin da sai Annabi (s.a.w) ko wasiyyin Annabi ne kawai zai iya yin su ko kuwa malami yana da dukkan dokoki a hannunsa ne gaba daya kamar yanke hannun barawo da jefe mazinaci da makamantansu? Ko mai dai me ye asali, mun tayar da wasu tambayoyin ne domin mu sanar da mai karatu cewa; akwai maganganu masu yawa a kasa a ajiye. Kuma wajibi ba ya saraya sai gwargwadon larura ko ilimi, sannan ihtiyadi da taka tsantsan shi na zaba a wadannan mas'aloli, akwai kuma dokar da take hararar mu da cewa duk wani hukunci da ya samu damar zartuwa ba ya saraya don wanda bai samu ba.

    Hafiz Muhammad

    Rajab 1430

    July 18, 2009