ArticleIDPicAddressSubjectDate
{ArticleID}
{Header}
{Subject}

{Comment}

 {StringDate}
 
 
 
 
 
 
 
ViewArticlePage
 
 
 
  • Tsarin Siyasa A Musulunci  
  • 2011. 10. 04 14:42:45  
  • CountVisit : 8  
  • Sendtofriend
  •  
  •  
  • Dandalin Siyasa

    Mece Ce Siyasa?

    Wasu Suna Cewa: Siyasa a dunkule ta kunshi jagorancin al’umma da tsarin tafiyar da al’amuransu (da yake cikin tsarin da dan’Adam yake a kansa a kasashe da ya hada da majalisar dokoki da ta yin doka (kotu) da ta zartarwa (wacce ministoci da shugaba suke cikinta).

    Ashe kenan muna iya cewa jagorancin al’umma a dunkule shi ne ake nufi da siyasa, kamar yadda kalma ce ta larabci da take nufin jagorancin al’umma da tafiyar da al’amuransu. Kodayake kada mu manta da yadda ake amfani da wannan kalmar da ma’anar yaudara, ko kuma sanya bangaranci a cikin warware wasu al’amura ko kuma kushe wani abu da ya fito ba daga namu bangaren ba, da makamantan hakan.

    Idan kana son ka gane hakan sosai duba yadda zabe yake a kasashenmu na Africa da yadda yake gudana, kai idan ina son in kawo misali duba ZIMBABWE a wannan kwanakin ka ga me yake gudana na tsananin zaluncin shugaba da neman mulki hatta da karfin tsiya, irin wadannan al’amuran duk ana kiransa siyasa musamman da yake ya shafi lamarin tafiyar da al’amuran al’umma koda kuwa ta kowace hanya ce. Kuma kungiyoyin da suke neman kaiwa ga wannan matsayin na rike ragamar tafiyar da kasa ana kiransu kungiyoyin siyasa.

    A nan ne fa aka fara maganar cewa; shin siyasa wani bangare ne na addini ko kuma wani abu ne daban da ba shi da alaka da addini? Kuma shin addini yana da wani matsayi da ya dauka a kan siyasa ko kuwa?

    A nan ne fa aka fara maganar cewa; shin siyasa wani bangare ne na addini ko kuma wani abu ne daban da ba shi da alaka da addini? Kuma shin addini yana da wani matsayi da ya dauka a kan siyasa ko kuwa?

    Idan mun duba tarihin rayuwar dan’Adam tun farkon samuwarsa yana tare da siyasa ne, sai mutum na farko ya kasance shugaba da zabin Allah a kan zuriyarsa, sai ya kasance annabi ne da yake karbar sako daga Allah (S.W.T) kai tsaye domin ya shiryar da shi kan yadda zai tafiyar da al’amuran jama’a a duniya, kai wani tunani da ya zo mini a kwakwalwata da na dade ina mamakinsa shi ne; cewar Allah (S.W.T) a farkon maganarsa game da dan’Adam da zai halitta ya fara ne da maganar siyasa yayin da yake gaya wa mala’iku cewa; zan sanya halifa a duniya. Halifa kuwa yana nufin mai maye gurbin Allah (S.W.T) a kowane abu a duniya da ya hada da tafiyar da al’amuran bayi wanda shi ne bangare mafi muhimmanci, domin kuwa shi ne ya shafi shiryar da dan’Adam kan al’amuransa na duniya da lahira.

    Duba ka gani yayin da Allah (S.W.T) ya ce da mala’iku: “Ni mai sanya halifa (mai wakiltata) a bayan kasa ne…” Bakara: 30. Da fadinsa: “Ya kai Dawud mu mun sanya ka halifa (mai wakiltar Allah cikin tafiyar da al’amuran bayi) a bayan kasa, sai ka yi hukunci tsakanin mutane da adalci…” surar Saad: 26.

    Da wannan ne zamu iya gane cewa tun farko addini yana damfare da siyasa kai tsaye, kuma tushen addini ya kafu kanta koda kuwa wasu daga malaman musulmi sun ki yarda da hakan.

    Amma dayawan ruwayoyi sun nuna mana ba yadda za a yi a cire jagoranci daga tushen addini, don haka imani da jagorancin annabawa (A.S) da kuma wasiyyoyi da wasiyyai (A.S) da suka bari yana daga tushen addini, kuma idan mutum bai yi imani da su ba koda kuwa ya fi kowa biyayya ga Allah a sauran bangarori Allah ba zai karbi ibadarsa ba, don haka ne ma duk wanda ya mutum bai san jagoran zamaninsa ba to ya yi mutuwar jahiliyya. (Minhajul karama, Allama Hilli, Shafi: 27). Domin zai zo a lahira babu wani abu da Allah zai karba na ayyukansa. Don haka yarda da manzon Allah (S.A.W) da wasiyyoyinsa da wasiyyansa (A.S) wanda ya hada da Kur'ani da halifofinsa (A.S) wadanda bai bar mutane ba sai da ya gaya musu wadannan halifofin nasa kuma ya fadi adadinsu cewa su sha biyu (A.S) ne kuma ya fadi sunanyensu sannan kuma Manzon Allah mai tsira da aminci ya gaya wa mutane ba zasu taba kauce wa hanya ba suna tare da Kur'ani har sai sun riske shi a tafkin alkausara a ranar lahira.

    Ashe kenan siyasa ita ce tushen addini da idan ma ba ka zama dan siyasa ba karkashin jagorancin da Allah (S.W.T) ya gindaya maka to kai ayyukanka ba zasu karbu ba har abada, zaka yi mutuwar jahiliyya ne. Don haka ne ma halifan manzon Allah (S.A.W) da ya yi wasiyya da shi na farko kuma jagoran Ahlul-bait (A.S) ya tambayi manzon Allah (S.A.W) bayan ya gaya masa kamar yadda al’ummar annabi Musa (A.S) da Isa (A.S) ba su bi wasiyyansu ba shi ma al’ummar nan ba zata bi shi ba, ya tambayi manzon Allah (S.A.W) cewa; zan yi wa al’ummar nan hukuncin kafirai ne ko kuma hukuncin wadanda suka fada fitina? Sai manzon Allah (S.A.W) ya amsa masa ya yi musu hukuncin wadanda suka fada fitina ne. Wannan kuwa lallai fitina ce, domin babu bala’in da ya kai ga cewa; Allah ba zai karbi duk ibadojin mutum ba!! A nan ne zamu samu natijar amsar tambayarmu cewa; shin addini yana tare da siyasa. Don haka muna iya gani cewa; asali ma tushensa ya doru ne kan siyasar.

    Amma tun da al’umma sun kauce wa siyasar Allah (S.W.T) da manzonsa (S.A.W) da wasiyyansa (A.S) kuma jam’iyyarsu mai cike da tsiran dan’Adam a duniya da lahira wacce take jam’iyya ce ta imani na gaskiya, to mene ne hukuncin sauran jagorori da ake rikonsu a matsayin shugabanni? Kuma mene ne sakamakon da ya samu al’umma sakamakon kauce wa siyasar Allah (S.W.T) da jam’iyyarsa. Kuma me ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan annabi (S.A.W) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa?

    Wannan sai ku biyo mu ba shi idan Allah ya sa mun samu lokaci a nan kusa…

    Amma tun da al’umma sun kauce wa siyasar Allah (S.W.T) da manzonsa (S.A.W) da wasiyyansa (A.S) kuma jam’iyyarsu mai cike da tsiran dan’Adam a duniya da lahira wacce take jam’iyya ce ta imani na gaskiya, to mene ne hukuncin sauran jagorori da ake rikonsu a matsayin shugabanni? Kuma mene ne sakamakon da ya samu al’umma sakamakon kauce wa siyasar Allah (S.W.T) da jam’iyyarsa. Kuma me ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan Annabi (S.A.W) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa?

    Musulunci addini ne na tsari wanda bai yarda dan’adam ya zauna haka nan babu daula ba, don haka ne ma ya kasance ya dauki matakin kiyaye tsarin rayuwar al’umma da yake akwai maslaharsu a ciki, sannan kuma sai ya shimfida dokokin da yake kiran su hukunci na biyu wadanda sun saba da na asali. Ina ganin domin fahimtar wannan al’amari yana da kyau mu kawo misalan wasu kissoshi da suka zo a littattafan addini:

    1. Wata rana Annabi Ibrahim (A.S) yana tafiya a gaban gwamnan da ya so ya kwace matarsa amma ya kasa, wanda daga baya ya ba shi kyautar Hajara babar Annabi Isma’il (A.S) sai suka fito suna tafiya gaban farfajiyar fadar gwamnan, sai Annabi Ibrahim (A.S) ya shiga gabansa yana tafiya, sai Allah madaukaki ya yi masa wahayi cewa; ya kai Ibrahimi (A.S) ka sani babu makawa al’umma ta samu shugaba Nagari ne ko fajiri; abin da ake nufi da nagari a nan Shi ne wanda Allah (S.W.T) ya zaba a shar’ance a matsayin jagoran al’umma, fajiri kuwa yana nufin duk wanda yake ba bisa wannan ka’ida ba.

    Sai gwamna ya ga Annabi Ibrahim (A.S) ya koma bayansa yana tafiya, sai ya tambaye shi me ya sa na ga ka koma bayana, sai ya ce: ubangijina ne ya yi mini wahayi da in girmama ka. Wannan al’amarin ya sanya shugaban ya ga girman Ubangijin Ibrahim (A.S) har ya karkato zuwa gareshi.

    Kissar Annabi Yusuf (A.S) ba nesa take da mu ba, a cikin kur’ani mai girma yayin da ya nemi a ba shi ministan arziki da albarkatun kasa, don haka ne ma wani wanda ya yi wa imam Rida (A.S) rashin kunya yana zarginsa da shiga  fadar sarki Ma’amun dan Harunar Rashid, sai imam Rida (A.S) ya ba shi amsar da ta sanya shi yin nadama, yana mai nuna masa cewa; tsakaninsa (A.S) da Annabi Yusuf (A.S) ya zabi wanda ya fi laifi a wurinsa yayin da shi imam Rida ya karbi sarautar Yarima ne bisa tilas, amma Annabi Yusuf (A.S) ya nemi ministan arziki da albarkatun kasan Misira yana mai rokon sarki ya ba shi wannan matsayi, sannan kuma Imam Rida (A.S) ya kasance a fadar musulmi ne masu shaidawa da Kadaitar Ubangiji madaukaki, yayin da Annabi Yusufi (A.S) ya zauna a fadar mutane ne da suke bauta wa gumaka!

    A nan ne zamu ga muhimmancin kare tsarin al’umma da kuma yin hidima ga al’umma da kiyayewa bisa adalci, mu sani imam Ali (A.S) yana cewa: “Mulki yana wanzuwa tare da kafirci amma ba ya wanzuwa tare da zalunci”. (sharhi usululkafi: Mazandarani, j 9, s 300.

    Sai dai wani yana iya tambaya cewa; me ya sa wadannan manyan bayin Allah (S.W.T) guda uku: Annabi Ibrahim (A.S) da Annabi Yusufi (A.S) da imam Rida (A.S) suka dauki wadannan matakai, ashe ba hakkinsu ba ne su rike jagorancin al’umma sai kuma suka dauki wadannan matakai a gaban wadannan sarakunan lokutansu?

    Sai mu ce: matakai ne da suke sassabawa da sabawar yanayi, don haka ne ma hukuncin Allah a kowane fage da ya hada da siyasa yake sassabawa, misali da Imam Hasan (A.S) ya zo lokacin Imam Husain (A.S) da zai yi yaki ne da Yazid, kamar yadda da imam Husain (A.S) ne a lokacin Imam Hasan (A.S) to da zai yi sulhu da Mu’awiya. Don haka ne mukan ga wani lokaci Annabi (A.S) ko Imami (A.S) ya dauki matakin da ya saba da na waninsa (A.S) kamar matakin Annabi Isa (A.S) a daular Rum da ya saba da matakin Annabi Musa (A.S) a daular Misira kafinsa da kusan shekaru 1100. Ko kuma Annabi daya ya daukin matakan siyasa da suka saba a lokuta biyu kamar yadda Annabi Ibrahim ya kira sarkin Babil a kan Tauhidi har ya kona shi, amma sai kuma bai yi wannan kiran ba ga sarkin Siriya da na Misira. Kuma muna iya ganin Imam Ali ya yi hakuri ya zauna lafiya da halifofin farko bai dauki matakin yaki ba, amma sai ya dauki wannan matakin tare da Mu’awiya, wanda da ya kyale tabbas da ya zama shugaba a zamaninsa shi ma bayan Usman dan Affan, kuma a zahiri yake wadannan matakai sun sassaba.

    Wani yana iya tambaya ya ce: To yaya zamu gane wadannan matakai sai in ce yana da wuya ka gane domin abu ne wanda yake bukatar shiriya daga Allah (S.W.T), kuma mutane sun ki yarda su karbi wannan shiriya don haka duk wani bala’in da suka fada su suka jiyo wa kansu, kuma duk da ba zamu iya ganewa ba saboda wahalar sanin wane yanayi ne, kuma wane mataki ne, kuma a wane lokaci ne, kuma waye zai yi, da sauran wahalhalu da suka dabaibaye wannan lamarin amma wasiyyin Annabi (A.S) na karshe ya zartar da matakan wadanda suka gaje shi suka san koyarwarsa suka dauki ilimi daga abin da ya bari suka kai matakin sani na koli duk da kuwa zai iya kasancewa cike da kurakurai, amma da yake bisa hasken doka ne don haka sai ya kasance kuskure ne wadannan manyan malamai zasu iya yi mai lasisi daga Allah, sabanin wani wanda ba a ba shi lasisi daga Allah ba ko Annabi (S.A.W) ko wasiyyin Annabi (A.S), kuma bai ma san koyarwarsu ba.

    Wahalar wannan al’amarin ta kai ga cewa; tun da ake tashi domin gwagwarmayar yakar sarakuna masu mulki a cikin sama da shekaru dari biyu da hamsin na wasiyyan manzo (S.A.W) har zuwa karamar boyuwar wasiyyinsa na sha biyu kuma halifansa na karshe da ya yi albishir da shi, ba mu samu wata gwagwarmayar siyasa ta kifar da daula ba da ta samu goyon baya daga wasiyyan Annabi (S.A.W) (A.S) sai ta Mukhtar da ya dauki fansa ga makasan imam Husain (A.S) shi ma ba yarda ta karara ba ce, sai kuma gwagwarmayar Zaid bn Ali tare da karfafawar da suka yi cewa; ba za a taba samun nasara ba, al’amarin da ya kai ga kashe dukkan wadanda suka tashi suka yi wannan motsin.

    Idan mun duba a fili yake cewa shugabannin addini na gaskiya da Allah da manzonsa suka ayyana sun riga sun bayar da matakan da ya dace a dauka na shiryar da al’umma zuwa ga tafarkinsu da tarbiyyarsu ga sanin Allah (S.W.T) da hakkokinsa da kuma hakkokin ‘yan’adam da kuma wadanda suka hau kansu, da kuma komawa zuwa ga malamai masu gadon tafarkinsu kawai banda sauran malaman da suke hana mutane saninsu kamar yadda suka kira su da sunan masu fashin imani wanda ya fi na rayuka da dukiyoyi muni. Kuma su ne zasu nuna yadda za a yi mu’amala da kowane mutum ne tun daga sarakuna da shugabanni da kowane jagoran wata al’umma ba tare da rikon su a matsayin su ne jagororinsu na shiriya ba, don haka rikon wani mutum daban jagora kuma shugaba mai shiryarwa ga tafarki sabaninsu to daidai yake da mutuwar jahiliyya!!!

    2- Amma abin da ya samu duniya sakamakon kauce wa siyasar Allah (S.W.T) da jam’iyyarsa wannan wani abu ne da yake a fili, muna iya ganin yadda duniyar dan’adam ta bace kan al’amarin duniya da lahira ta fada cikin alakakai da surkukiya; amma al’amarin lahira a fili yake cewa mutane sun kasa sanin addinin gaskiya ko mazhabar gaskiya suna ta dimuwar da ta fi dimuwar shekaru arba’in ta Banu-Isra’ila muni, domin dimuwar yau ta rashin sanin gaskiya ce, wannan kuwa sakamakon ‘yan fashi da suka yi yawa a kan hanyar isa zuwa ga Allah madaukaki ne, sannan kuma dimuwa ce da ba wanda ya san sanda zata kawo karshe. Don haka kamar yadda suka dimauce kan al’amarin lahira ta yadda suke bin kowane irin kira doo. Haka nan ma suka dimauce kan lamarin duniyarsu ta yadda babu wani wanda ya isa ya fitar da duniya daga dimuwarta ta al’adu da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da tarbiyya da makamancinsu ta yadda zai fito da ma’anar adalci a kowane fage wanda yake nufin gaskiya a komai ba tare da tauyewa ba sai wanda yake ya san Allah (S.W.T) hakikanin sani wanda kuma babu wani wanda yake haka sai wanda Allah (S.W.T) ya zaba na annabi (S.A.W) ko kuma wasiyyinsa (A.S), amma su ma da sharadin al’umma ta yarda da jagorancinsu.

    Amma abin da ya yake cikin tunanin wasu masu ganin cewa don me ya sa Annabi (S.A.W) ko kuma imami (A.S) bai dauki wasu matakai ba na shari’a? sai mu ce duk wannan yana komawa ne zuwa ga rashin yardar mutane; Misali me ya sa jagororin da manzon Allah (S.A.W) ya yi wasiyya da su ba su riki jagoranci ba? Sai mu ce: yana daga sharuddansu mutane su yarda da su sannan sai su riki jagorancin al’umma. Muna iya ganin yawancin annabawa (A.S) ba su riki jagorancin al’umma ba na tafiyar da mulkinsu saboda al’ummar ba ta yarda ba, don haka ne ma zabe yake da muhimmanci a wannan zamani namu, kuma shari’a ta ki yarda da wani ya jagoranci mutane koda kuwa annabi (A.S) matukar mutanen ba sa so.

    Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Allah ya tsinewa mutumin da ya jagoranci mutane alhalin ba sa sonsa.

    Don haka ne ma imam Ali (A.S) ya ki jagoranci saboda mutane ba su zabe shi ba, amma da suka zabe shi ya riki mulki kuma da wani ya tashi domin ya kwata daga gareshi sai ya yake shi da mutanen.

    Mulki a hannun bayin Allah (S.W.T) nagari da ya zaba ita ce hanyar shiryar da bayi, don haka idan suka ki Allah madaukaki bai yarda a tilasta su ba. Amma kuma idan mutane suka ki yarda da zabin Allah (S.W.T) -duk da Allah ya kyale su bai yarda a tilasta su karbar wanda ba sa so ba- amma bala’o’in duniya da na lahira zasu durfafe su.

    Mu duba mu gani mana a lokutan jagorancin manzon rahama (S.A.W) da imam Ali (A.S) ba a taba samun wani ya mutu da yunwa ko talauci ba, kuma ba a samu yawaitar jahilci da rashin tsaro ba, kuma ba a samu karancin abinci da yunwa ba saboda tsarin da suka zo da shi a hukumarsu duk da kuwa kowannensu hukumarsa cike take da yake-yake!

    Muna iya gani abin da imam Ali (A.S) ya yi yayin da ya ga wani tsohon bayahude a hanya a Kufa yana bara sai ya tambaya ya ce: me ye haka! Mu duba mu gani bai ce wane ne wannan ba, sai ya ce mene ne wannan, wato bakon abu ne a daularsa a samu bara. Sai ya yi fada kan cewa; wannan bayahuden ya yi wa mutane ayyuka yana saurayi sai da ya tsufa sannan sai a kyale shi!? sannan ya sanya masa albashi daga Baitul mali!

    Me kuwa zai sanya dan’adam ba zai wahala ba alhalin ya kauce wa tsarin da zai fisshe shi daga bala’in duniya da lahira, mu sani duk duniya babu wani wuri da ake bin tsarin addinin musulunci kamar yadda Allah (S.W.T) da manzonsa (S.A.W) suka zo da shi, wani wurin ana gaba da addini ne, wani wurin kuma ana jahiltarsa ana yin wani abu daban da sunan addini amma addini ba haka ya ce ba, ba komai ake yi ba sai fahimtar mutanen wurin game da addini. Wani wurin kuma an fahimci addin kamar yadda manzo (S.A.W) da wasiyyansa (A.S) suka zo da shi, amma fa al’adu sun hana a aiwatar da shi. Wannan sai ya sanya duk duniya ba inda ake yin addini koda kashi 50% cikin dari a duk fadin wannan duniyar.

    Wasu sun dauka an zo duniya domin shan wahala ne don haka sai suka dauka wahalar da ake sha da ma haka duniya take! wannan lamarin kuwa ya taso daga jahilcin dan’adam ne, ko kuma daukar da ya yi wa abin da yake faruwa kamar daman haka ya dace ya faru! Mu sani duniya da lahira duka an yi su domin samun kamalar dan’Adam ne, bambancin al’amarin shi ne akwai wahalar ibada a wannan duniya. Kuma rashin lafiya da cututtuka duka Allah ya bayar da maganinsu sai dai dan’adam ya nisanci wanda zai yi masa maganin ne. Sannan muna ganin yadda manzon Allah (S.A.W) da imam Ali (A.S) suka yaki talauci da yunwa ta karfin tsiya da kuma kawo aminci da ilimi da tarbiyya da sauransu. Imam Ali (A.S) yana cewa: Da talauci mutum ne da na kashe shi (Sharhu Ihkakul hakk: J 32, shafi: 257)

    Arzikin duniya ya ishi dan’adam amma ya wanzu a bankunan masu mulki da iko ana boye shi ana juya shi, kuma wannan lamarin shi ne abin da Allah ya yi gudunsa yana mai cewa; “…domin kada ya kasance yana juyawa tsakanin mawadata daga cikinku…”(Hashari: 7), amma dan’adam da aka yi arzikin saboda shi sai ya kwana cikin yunwa da musibu da talauci.

    Amma batun cewa; me ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan annabi (S.A.W) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa?

    Kuma me ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan annabi (S.A.W) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa?

    3- Amma abin da ya kamata wannan al’ummar ta yi game da jagoran gaskiya kuma halifan annabi (S.A.W) na sha biyu da yake wannan ne zamaninsa shi ne ta koma zuwa ga koyarwarsa, ta san wane ne shi sannan sai ta san wadanda ya ce ta koma musu wajen sanin addininsu, to da wannan ne zasu iya zama ‘yan jam’iyyar Allah madaukaki.

    Da wannan ne zasu koma zuwa abin da ya fada a littafinsa: “Kawai hukunci na Allah ne” (al’an’ami: 57). Da fadinsa: “…Hukunci nasa ne…” (al’kasas: 88). Da kuma dukkan ayoyin da suka yi nuni da fasikanci ko kafirnci ko zaluncin wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, da wannan ne sai su aikta ayyukan da suke kansu na mu’amala da dukkan wani dan’adam bisa yadda shari’a ta ce musu kamar yadda ya zo daga wajen Allah madaukaki. Sai ya kasance alakokinsu da kowa bisa yadda Allah ya so ne kuma jagoransu na wannan zamani ya tsara ya nuna musu. Da wannan ne zasu kasance ‘ya’yan jam’iyyar Allah madaukaki wacce take da sakamakon yardarsa duniya da lahira.

    Irin wadannan malamai da suke bin tafarkin Allah madaukaki da manzonsa (S.A.W) da wasiyyansa (A.S) su ne wadanda manzon rahama (S.A.W) yake cewa: “…hakika malamai magada annabawa ne” (kafi: j2, sawabul ilm, hadisi: 1) da fadin imam Ali (A.S) cewa; “Malamai su ne masu jagorancin mutane” (Gurarul hikam: 137), da fadin manzon Allah (S.A.W) da yake nuna cewa; idan malamai suka bata to zasu batar da wannan al’umma.

    Wani abin mamaki shi ne yadda wasu malamai suka ki fahimtar al’amarin jagoran al’umma bisa gurbatacciyar fahimta sakamakon kaucewa wasiyyar da annabi (S.A.W) ya yi na su bi abin da yake kunshe cikin Kur’ani bisa fahimtar  ahlin gidansa (A.S) wadanda Allah madaukaki ya tsarkake su kuma manzon Allah (S.A.W) bai bar wannan duniya ba sai da ya yi wasiyya da su kamar yadda muka yi nuni a baya da halifofinsa goma sha biyu ne kamar yadda ya kawo su kuma ya yi wasiyya da su.

    Wani abin mamaki shi ne yadda wasu sukan yi kokarin su boye wasiyya ko su yi musunta, ko kuma su daukar wa kansu yarda da cewa; manzon Allah (S.A.W) ya fadi sha biyu amma bai kawo sunayensu ba, don haka sai su shiga neman kawo sunayen da kansu kamar dai Allah ya yi wahayi cewa; manzonsa (S.A.W) ba zai cika addininsa su ne zasu zo daga baya su cika. Irin wannan son rai yana nan kunshe cikin littattafai daga wasu masu irin wadancan mahanga ta su cika addini da kansu! Allah ya tsare mu tabewa!

    Mu sani cewa; tafiyar da al’amarin siyasa da jagorancin al’umma abu ne na wadanda Allah ya zaba ya mika musu ya sanya shi a hannunsu wadanda muka ce imma dai annabi (A.S) ko kuma wasiyyin annabi (A.S) idan kuwa ba haka ba to wanda ya hau wannan mahalli a wajen Allah sunansa fajiri fasiki komai kuwa takawarsa ta zahiri, domin ma’aunin da muke hange da shi, shi ne dai ma’aunin da Allah yake hange da shi.

    Idan kuwa yana son kada wannan suna ya hau shi to kada ya sake ya hau wannan mataki sai idan annabi (A.S) ko wasiyyin annabi (A.S) ko kuma wanda wasiyyin annabi (A.S) ya ce ya hau wannan matsayin sakamakon ba a gane shi a fili koda kuwa an gan shi, sai ya mayar da mutane zuwa ga malamai masu wasu siffofin da shi ya ayyana su da kansa da shiryarwar ubangijinsa madaukaki da kuma ta annabin rahama (S.A.W).

    Imam Ali (A.S) yana cewa da alkali shuraihu: Ya shuraihu ka zauna a mazaunin da babu mai zama a wurin sai annabi (A.S) ko kuma wasiyyin annabi (A.S) ko kuma tababben tsinannen mutum (al’wasa’il: babin hukunci: babi 2, h 2, shafi: 6). Kamar yadda imam sadik (A.S) yake cewa: Ku ji tsoron mulki domin shi mulki na malami ne masani da hukunci da adalci wanda yake shi ne annabi (A.S) ko kuma wasiyyin annabi (A.S) (Daga al’wasa’l: kamar na bayansa). Don haka ne ma ake fassara ma’anar malamai a irin wadannan hadisai da annabi (A.S) ko kuma wasiyyin annabi (A.S).

    Amma hanzari ba gudu ba: Dayawan malamai sun tafi a kan cewa; idan aka samu wani mumini da yake karbar shawara daga malamai wadanda suke kan tafarkin manzon Allah (S.A.W) da koyarwarsa sahihiya (A.S) ya kasance yana karbar shiryarwa da yadda zai tafiyar da al’amuran al’ummarsa daga garesu to wannan ya fita daga cikin wannan tabewa kuma irin wadannan mutane ba sa ciki saboda su ma yanzu suna karkashin umarnin Allah da manzonsa da wasiyyansa da kuma malamai mabiyansu ne, kuma sun fita daga sunan fajirci, ko dagutanci.

    Kamar yadda malamai suka yi fahimta ga hadisin da yake cewa duk wata tuta da aka daga (wato duk wata gwagwarmaya da ake yi) kafin bayyana Sufyani to ta dagutu ce (wato; ba halattacciya ba ce), wasu malamai sun tafi a kan hakan, amma muna iya ganin imam khomain (K) jagoran juyin musulunci a Iran a 1979, yana ganin hadisin bai hada da tutar da aka daga kuma ta kasance ba ta saba da koyarwarsu ba, sai ya kasance kenan ya halatta malamin da yake bin hanya sahihiya da sharadin ya samu lasisin wasiyyan annabi (A.S) zai iya yin wani motsi bisa sharuddan da suka gindaya. Sai ya kasance wannan kauce hanya bai hada har da shi ba. Wannan dai mas’ala ce mai girma da ta tayar da jijiyar wuya saboda santsinta da kuma wahalarta kamar yadda dai sauran mas’alolin siyasa suke. Kuma nan ba zauren karatu ba ne balle mu fadada magana.

    Shin ya halatta domin gudun hukumar dagutanci mutane su zauna babu shugaba sam?

    Wane irin shugabanci ne a duniya yake da inganci idan mun yi la’akari da yadda abubuwan suke wakana?

    Wannan sai ku biyo mu bashi idan Allah ya sa mun samu lokaci a nan kusa…

    Shin ya halatta domin gudun hukumar dagutanci mutane su zauna babu shugaba sam?

    Wane irin shugabanci ne a duniya yake da inganci idan mun yi la’akari da yadda abubuwan suke wakana?

    1- A amsa ta farko muna iya ganin a fili yake daga abin da ya zo a koyarwar musulunci shi ne; bai halatta ba mutane su zauna babu jagora da shugabanci, don haka wajibi ne su samu shugaba ta fuskancin wajebcin kiyaye tsarin al’umma. Sannan kuma wannan yana daga babin ture fasadi babba da fasadi karami ne, don haka ne ma imam Ali (A.S) yake cewa; dole ne a samu shugaba ga mutane nagari ne ko fajiri. Kuma mun riga mun yi nuni da ma’anar fajiri a nan da cewa; yana nufin wanda ba bisa dokar asali ta Allah (S.W.T) yake jagorantar mutane ba, wato jagorancinsa babu lasisi daga Allah madaukaki mai kowa mai duka.

    Don haka ne ya wajaba a girmama wannan shugaban koda kuwa ba bisa ka’ida yake ba, sai dai idan ya yi umarni da saba wa Allah madaukaki, to a nan ba za a bi shi ba. Kuma idan zabi ya kasance tsakanin samun wannan jagora da rashin jagora dole ne mutane su yi riko da jagorancinsa su kuma yi kokarin samar da wannan tsarin. Kuma kokarin kawar da wannan tsarin ta yadda zai kai ga mutane ga rasa wannan tsarin saba wa ne.

    Amma shugabanci da muke gani na kungiyoyi ba ya cikin abin da ake magana a kansa, domin shi ya doru ne bisa “…Ku yi taimakekeniya a kan kyakkyawa da takawa, kada ku yi taimakekeniya a kan sabo da ketare iyake…”. Don haka duk sa’adda wasu mutane suka hadu suna iya kafa kungiya ta ayyukan alheri ta yadda zasu taimaka wa al’ummarsu ta hanyoyi da dama, ilmantarwa, kula da lafiya, kula da tsaron yankunansu, gyaran hanya, da hanyoyin ruwa, da titian, da kafa cibiyar motsa jiki da wasanni da makamantansu. A nan mutane suna iya kafa dokokin da suke na maslahar zamantakewarsu da kuma tafiyar da kungiyarsu bisa kyakkyawa matukar dokokin ba su saba wa kykkyawar al’ada ko addini ba. Irin wannan shugabanci abu ne da mutane mahankalta suka hadu a kan samar da irinsa kuma shari’a ta zartar da shi matukar bai kai ga keta dokokinta ba.

    2- Kafin mu bayar da amsa ta biyu muna iya cewa; akwai nau’o’in shugabanci a rayuwar ‘yan’adam kamar haka:

    a. Na addini; kuma ya hada da: 1) wanda Allah ya yarda da shi kamar na annabawa (A.S) da wasiyyansu (A.S) da kuma wadanda wasiyyansu suka ba su lasisin jagorancin al’umma ta hanyar ayyana su kai tsaye ko kuma ba kai tsaye ba, kamar su fadi siffofin mutanen da suke iya jagorantar mutane kamar yadda wannan yake kunshe cikin littattafan addinai. 2) Da kuma wadanda ba su cancanta ba bisa dokar addini sai dai sun zo da sunan addini ne suka kwace mulki ta karfin tsiya. Ko kuma sun samu karbar jagorancin al’umma amma bisa gurguwar fahimtar addini wacce ba sahihiya ba.

    b. Na zabin al’umma: da ya hada da tsarin zabin gwamnati ta hannun al’umma kamar Demokradiyya, ko kuma tsrin jamhuriyya, da tsarin taho mu kafa gwamnati daya daga bangarorin wasu kasashe ko kuma daga kasashe daban-daban da makamantansu.

    c. Na kungiya kamar yadda kwaminisanci yake danne sauran al’umma ya sanya iko a hannun ‘ya’yansa kawai da karfin tsiya.

    d. Na wasu jama’a takaitattu saboda kawai suna da karfi ko ikon yin hakan kamar yadda sojoji sukan yi a kasashen duniya.

    e. Na gado kamar sarakuna da ake da su a kasashen duniya, kuma tsarin ne da babu wani ma’aunin kasancewar jagora shugaba sai domin kawai an haife shi daga wani gida sai ya gaji babansa. Kuma shi ma ya kasu gida biyu: imma dai mai sarki kawai, imma kuma mai sarki amma da majalisa.

    To dukkan wadannan tsarurrukan duka ba su inganta ba sai dai na farko shi ma wanda Allah ya ayyana da kansa, don haka duk sauran tsarurruka a mahangar addini ba su da kyau, muna ganin yadda sheikh Usman dan Fodio ya kyamaci mulkin sarauntar gado kuma ya kira shi da bidi’a don haka masu sukan sa ina ganin ba su yi mishi adalci ba domin an mayar da ita gado ne bayan mutuwarsa, Idan mun duba a cikin littafin Shehu Usman dan Fodio na “Najmul ikhwan Yahataduna bi iznil-Lahi Fi umurizZaman” zamu ga yadda yake kyamatar wannan tsarin har yana nuni da cewa; Farkon wanda ya bata al’amarin al’ummar musulmi shi ne Mugira bn Shu’uba yayin da ya ba wa Mu’awiya shawarar ya sanya dansa Yazid kan mullki. Kuma mun ga yadda dayawa daga sahabbai da ‘ya’yansu suka kyamaci abin da Mu’awiya ya yi na sanya Yazid dansa kan mulki har ta kai ga jayayya da barazana da Mu’awiya ya yi na fille kan su Abdullahi bn Umar da sauransu idan ba su yi wa dansa bai’a ba.

    Haka nan sayyid Ra’is Zadeh yana cewa: “Ban taba ganin wani nau’in tsari da imam Khomain (K) yake kin sa ba irin tsarin gadon mulki”. Ya ce: “A bisa wane dalili ne kawai don an haife ka a wani gida shi kenan sai ka zama jagoran al’umma koda kuwa ka fi kowa dolanci”.

    Idan muka ga Allah ya zabi wani to ba doming gado ba ne, sai dai domin ya fitar da zuriya mai tsarki daga gida mai tsarki kamar yadda ya yi wa alayen Ibrahim; kamar annabi Is’ma’iI da Is’hak (A.S), ko kuma alayen Imrana wanda su ma annabawa ne da wasiyyansu, ko kuma annabi Dawud da Sulaiman (A.S) ko kuma abin da ya yi wa alayen Muhammad (S.A.W) wanda ya hada tun daga dan’uwansa Ali (A.S), kuma ya sanya zuriyarsa tsarkaka sha daya daga gareshi da shi da ‘yarsa Fadima (A.S) tun daga Hasan (A.S) har zuwa Mahadi (A.S). Wannan kuwa ya yi kamar yadda mutum yake kera motoci sai ya yi wasu masu shakali mai kyau da jan hanakli wasu kuma sai ya yi su masu saukin kudi da karancin jan hankalin mutane da karancin inganci. To haka nan Allah mai hikima yake yin halittarsa da bambanci yadda ya so, don haka ne ma kamar yadda mai yin mota ya yi wata tana da karfi da gudun 280, wata kuma ya yi ta da rauni da gudun 120, sannan kuma ba ya ganin laifin mai 120 domin ta kasa gudun mai 280. To haka nan Allah mai hikima ya yi mutane; sai ya yi annabawa (A.S) da wasiyyansu ya yi su ma’asumai saboda ya ba su ilimin hakkun yakin da ainul yakin da ilmul yakin ta yadda suna iya ganin gaskiya kamar yadda take. Amma sai ya yi sauran mutane da yawanci sun rasa hatta da ilmul yakin balle su kai ga ainul yakin balle kuma karshe hakkul yakin. Don haka ne ma bai dora wa su sauran mutane nauyin da ya kai na wadancan masu daraja ba.

    Sannan kada mu manta cewa; duk da Allah madaukaki ya ba wa annabawa da wasiyyansu (A.S) ikon tafiyar da al’umma amma bai ba su ikon tilasta mutane su bi su ba, sai ya ba wa al’umma zabi idan sun zabe shi to ya kafa hukuma, amma idan ba su zabe shi ba ya ci gaba da shiryar da su daidai gwargwadon abin da zai iya yi kamar yadda dai muka riga muka yi bayanai a baya. Wannan kuwa a cikin maganganun imam Ali (A.S) musamman a Nahajul Balaga muna iya fahimtar hakan, hada da abin da ya zo na tarihi a cikin littafin Kur’ani mai girma da ruwayoyin manzon Allah (S.A.W). Al’amarin hukuncin bin Allah bisa tilas ko bisa zabi da biyayya zai wakana ne da bayyanar Imam Mahadi (A.S)!

    Mene ne sharuddan jagora da ayyukansa?

    Sharuddan jagora a takaice kamar yadda na yi wani bincike a kai sun hada da:

    Mai yawan Ilimi kuma masani kan abubuwan da suke gudana; mai cikakken hankali; mai kyawun jagoranci; mai adalci; mai takawa; mai gaskiya; mai madaidaiciyar dabi’a; mai karfi; mai dacewa; mai lafiya; mai yin shawara; masanin zamaninsa da addininsa; masanin al’amuran tafiyar da al’umma; wasu sun kawo ya kasance namiji; mai ba wa kowa ‘yanci da daidaito; mai daidaita kowa a gaban doka; mai duba bukatun mutane; mai biyan bukatun talakawa; mai daidaito a bayarwa; mai kyakkyawar mu’amala; mai tarbiyyantar da al’umma; ya kasance baligi; mai gabobin masu lafiya; kada ya kasance dan zina; ya kasnce da ba bawa ba; ya kasance ba ta karfi ya hau mulki ba; mai kwarjinin da idan ya yi umarni za a bi; mai tausayi; mai kariya ga kasa da al’umma; mai kusanto da talakawa kusa da shi; mai yafewa tare da yana da iko; mai kyautata wa kowa; mai game kowa a cikin al’amarin kasa da hakkoki; kada ya kebanci na kusa da shi da arzikin kasa; mai farkawa kan komai; mai tsananin kiyayya da zalunci; mai kankanda kai; mai kyakkyawar zuciya; kada ya kasance fajiri ko faskiki; mai kula da muhimmantar da al’amuran al’umma; mai zabar maslahar al’umma kan maslaharsa; mai nasiha ga mutane; mai yalwata musu rayuwarsu; mai hakuri matuka da juriya; mai iya bayani; mai ilmantarwa; mai koyar da tarbiyya; amintacce ba mai cin amana ba; mai ikhlasi da sadaukarwa; mai karfin imani da kyawawan halaye; mai sauraron kukan jama’a da kokarin warware matsalarsu da gaggawa; mai tsananin tsoron Allah; mai biyayya ga dokokin Allah; mai ayyuka nagari; mai karfin zartar da umarnin Allah sabanin son ransa; mai tsayar da haddi koda kuwa kan nakusa ne; maras tasirantuwa da sanayya; mai tsananin tausayi da yin afuwa ga mai laifin da shari’a ta ba shi damar yin afuwa; mai kauna da rige zuwa ga tafarkin Allah; mai yalwar kirji da tunani; mai kaifin kwakwalwa; mai karbar nasiha a boye da sarari; wanda ba ya daukar fansa kan abokan hamayya; mai bin hanyar daidai wajen ayyukansa babu yaudara; mai amsawa bukatun al’umma; mai amsa kiran al’umma; maras kwadayin duniya da kyale-kyalinta; mara zari da handuma; maras cin amanar al’umma; mai kame kai; mai kunya; mai karimci da kyauta; mai nuna daidaito ga al’umma; maras tsoro; maras rauni; mai hikima; maras dimaucewa; maras kwadayin shugabanci; maras raunin siyasa; mai kyakkyawan shugabanci; mai iya tafiyar da al’amuran al’umma da kyau; mai sanya tausasawa a ayyukansa; mai duba farko da tsakiya da karshen abu kafin ya aiwatar; mai kula da yardar al’ummarsa; mai tsantseni; mai tarbiyyar kansa da yi wa kansa hisabin ayyukansa a kullum; mai karbar shawara; .

    Ayyukan jagora:

    Kare addini da isar da shi; gyara al’amarin mutane; raya sunna; tsayar da haddodi; kokarin ayyukan alheri; yin wa’azi da shiryarwa; yada adalci ga al’umma; yakar makiya da kare al’umma; karbar hakkokin Allah; ayyana shugabannin ayyuka ko cire su; kiyaye hakkokin al’umma; raba arzikin kasa da hidima ga mutane; yin shawara da mutane; nisantar fushi; jawo yardar mutane; raya addini; kula da hakkokin raunana da marasa rinjaye; bayar da ‘yancin bayani da suka; alaka da mutane; kula da ayyukan tausaya da jin kan raunana wato miskinai da talakawa; kiyaye tsaron al’umma; kiyaye dukiyar al’umma; kiyaye kasuwanci da hana boye kaya; raya kasa da gine-gine domin samar da kowa gidan zama; yakar talauci; samar da aminci; yada kyawawan halaye; sanya shugabannin ayyuka nagari salihai; jarrabawa ga wakilai kafin ba su ayyuka muhimmai kamar jarraba amanarsu da kunyarsu da kamewarsu; samun mutanen da suka fito daga gidaje nagari domin ba su ayyuka muhimmai kamar wakilci, kula da addinin wanda zai ba shugabanci; sanya ido kan ma’aikatansa; yi misi hisabi mai tsanani; karfafa su da kuma yi musu gargadi; hukunta su idan sun saba;

    Saboda kasancewar muna son daukar hutu in Allah ya so wannan bahasin da yake yana da tsayi zamu cigaba da shi nan da wata uku;

    Sannan kuma in Allah ya so zamu kawo bayanai game da Imam mahadi (A.S), kodayake kusan shekara guda kenan (idan ban manta ba) rajab ko sha’aban ko Ramadan na taba ganin wani ya buga wasu bayanai da muka sanya a wani sayet da kuma wanda muka buga a game da Imam mahadi (A.S) a wata jarida ta musulunci ta hausa amma sai ya sanya sunansa kawai, ina ganin a rika kiyaye amanar ilimi a rika fadin inda aka nakalto kasidoji! Hafiz Muhammad Sa'id Kano, Cibiyar Al'adun Musulunci, August 2008

     
    FirstName :
    LastName :
    E-Mail :
     
    OpinionText :
    AvrRate :
    %0
    CountRate :
    0
    Rating :