f) – Zagin Mumini da Bata Masa Suna
Daga ciki har da zagin mumini ko la’antarsa ko bata masa suna. An ruwaito wani hadisi daga Abil Hasan Musa (a.s) kan wasu mutane biyu da ke zagin junansu, inda ya ce: “Wanda ya fara daga cikinsu shi ne yafi zalunci, laifinsa da laifin dayan na wuyansa matukar bai nemu gafarar wanda aka zalunta ba”.
Abu Ja’afar (a.s) yana cewa: “Wani mutum daga kabilar Bani Tamim ya zo wajen Ma’aiki (s.a.w.a) ya ce: ka yi min wasiyya, daga cikin abin da ya masa wasicci da shi har da cewa: Ka da ka zagi mutane, sai ka samar da kiyayya gare su”.
Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Allah Madaukakin Sarki Ya halicci mumini ne daga girman daukaka da kudurarSa, duk wanda ya bata masa suna ko ya mayar masa da magana, to ya mayar wa Allah ne”.
Daga wajensa (a.s) ya ce: “Idan la’ana ta fita daga ma’abucinta za ta yi yawo tsakaninsa da wanda aka la’antar, idan ta samu wajen zama shi kenan idan kuwa ba ta samu ba sai ta koma wajen mai ita, shi ya fi dacewa da ita. Don haka ku guji la’antar mumini don kada ta fada kanku”.
g) – Cin Naman Mumini
Daga ciki har da ambaton mumini a bayansa da abin da ba ya so, da kuma bayyanar da aibinsa da ya boye, shi ne abin da ake kira da ‘giba’ (cin nama) da Alkur’ani ya bayyana haramcin a fili, inda ya siffanta shi da cin naman mamaci “…kuma kada sashenku ya yi gibar sashe. Shin, dayanku na son ya ci naman dan’uwansa yana matacce? To, kun ki shi…”.
Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Wanda ya fadi wani abu kan mumini daga abin da idanuwansa suka gani ko kuma kunnuwansa suka ji, to yana daga cikin wadanda Allah Madaukakin Sarki Ya fadi dangane da su cewa: Lalle ne wadanda ke son alfasha ta watsu ga wadanda suka yi imani, suna da azabamai radadi”.
Cikin wasiyyar Manzon Allah (s.a.w.a) ga Abu Zar, yana cewa: “Ya Aba Zar! Ina gargadinka da giba, saboda giba ta fi zina tsanani”, sai na ce: Saboda da me Ya Rasulallah? Sai ya ce: Saboda mutum ya kan yi zina ya kuma tuba Allah Ya karbi tubansa, ita kuwa giba ba a yafe ta har sai wanda aka yi ta a kansa ya yafe. Ya Aba Zar, zagin musulmi fasikanci ne, kisansa kuwa kafirci, cin namansa kuwa na daga cikin sabon Ubangiji, haramcin dukiyarsa tamkar haramcin jininsa ne. Sai na ce: Ya Rasulallah, mece ce giba? Sai ya ce: Ambatonka ga dan’uwanka da abin da ba ya so, sai na ce Ya Rasulallah, ko da yana da wannan abin da aka ambata din? Sai ya ce: Ka san cewa idan har ka ambace shi da abin da yake da shi ne ka ci namansa (giba), idan kuwa ka ambace shi da abin da ba shi da shi ne, ka zalunce shi”.
Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Wanda ya yi mu’amala da mutane bai zalunce su ba, ya kuma yi magana da su bai musu karya ba sannan ya yi musu alkawari bai saba musu ba, yana daga cikin wadanda gibansu ta haramta, kuma mutumcinsa ya cika, adalcinsa ya bayyana sannan ‘yan’uwa da shi ya wajaba”.
Malaman fikihu sun gibar fasiki mai bayyanar da fasikancinsa a fili cikin gibar da ta haramta. Daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Idan fasiki ya bayyanar da fasikancinsa a fili, to babu haramci gare shi da kuma giba”.
Abul Hasan (a.s) yana cewa: “Wanda ya ambaci wani mutum a bayan idonsa da wani abin da ke tattare da shi wanda kuma mutane suka sani bai yi gibansa ba, wanda kuma ya ambace shi a bayan idonsa da abin da yake tare da shi amma mutane ba su sani ba, ya yi gibansa, wanda kuwa ya ambace shi da abin da ba shi da shi ya kirkiri karya gare shi”.
h) – Kirkirar Karya
Babu shakka kirkira karya a kan mumini zalunci ne mai girman gaske da har ya fi giba girma, an ruwaito wani ingantaccen hadisi daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Wanya ya kirkiri karya ga mumini ko mumina kan abin da ba ya cikin halayensu, Allah Zai tura shi cikin Dinat Khibal har abin da ya fadi ya fice, sai na ce: mene ne Dinat Khibalkuma? Sai ya ce: Diwan da zai dinga fita daga farji….”.
i) - Annamimanci
Daga cikin hakan, har da annamimanci da bata alakar da ke tsakanin muminai da raba kawukansu. An ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani ingantaccen hadisi yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Ashe ba zan ba ku labarin mafi sharrin cikinku ba? Sai suka ce na’am Ya Rasulallah, sai ya ce: su ne masu yawo da annamimanci, masu raba tsakanin masoya, masu sanya aibi da maras shi cikin zalunci”.
Manzon Allah (s.a.w.a) cikin wasiyyar da ya yi wa Abu Zar (r.a) yana cewa: “Ya Aba Zar! Al-Kattat ba zai shiga Aljanna ba, sai na ce: Ya Rasulallah, wane ne kuma al-Kattat? Sai ya ce: “annamimi. Ya Aba Zar, annamimi ba zai taba hutawa daga azabar Allah ba a Ranar Kiyama. Ya Aba Zar, ma’abucin fuskoki da harsuna biyu a duniya zai kasance ma’abucin fuskokin biyu a wuta. Ya Aba Zar, (ka) zauna da (mutane) cikin amana, bayyanar da sirrin dan’uwanka ha’inci ne, ka nesanci hakan, ka nesanci zama da mai neman (aibin mutane)”.
j) – Tuhuma
Daga cikin hakan har da tuhumar mumini, ko kuma mummunan zato gare shi.
Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Idan wani mumini ya tuhumci dan’uwansa imani(nsa) zai narke cikin zuciyarsa kamar yadda gishiri ke narkewa cikin ruwa”.
Daga wajensa (a.s) yana cewa: “Amirul Muminina (a.s) cikin wani zance nasa yana cewa: Ka bar aikin dan’uwanka a mafi kyaun yanayinsa, har sai wani abin da zai kawar da hakan ya bayyana maka, kada ka yi mummunan zato ga duk wani kalami da ya fito daga dan’uwanka, matukar za ka iya ba shi wata fassara ta alheri”.
CIKAKKUN MISALAN ADALCI CIKIN AL’UMMA
Allah Madaukakin Sarki da Ahlulbaiti (a.s) sun jaddada jaddadawa mai karfi kan aiwatar da adalci cikin alaka ta zamantakewa tsakanin al’umma, saboda irin muhimmancin da hakan ke da shi wajen ginin al’umma.
A nan za mu yi ishara da wasu daga cikin misalan da ke nuni da hakan:
a) - Ganawa
Shari’a ta hana ganawa da yin magana kasa-kasa ko kebancewa tsakanin mutane biyu matukar akwai wani mutum na uku a tare da su. Alkur’ani mai girma ya aibata wannan aiki a kan wasu mutane da suka koma yin hakan bayan ya hane su ga hakan: “Ashe ba ka ga wadanda aka hane su ba daga ganawar, sa’an nan suna koma wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma suna ganawa game da zunubi da zalunci da saba wa Manzon Allah…”.
An ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani ingantaccen hadisi yana cewa: “Idan har mutane uku suka kasance waje guda, kada biyu daga cikinsu su kebance (ganawa) ba tare da na ukun ba, saboda akwai cutarwa da bacin rai cikin hakan gare shi”.
b) – Karkasa Lokaci
Yana da kyau idan mutum yana magana da mutane ko kuma yana zaune da su da ya karkasa lokacin tsakaninsu daidai wa daida. An ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani hadisi yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance ya kan raba lokacinsa tsakanin sahabbansa, ya kan dubi wannan da wancan daidai wa daida. Ya ce: Manzon Allah (s.a.w.a) bai taba mike kafafunsa tsakanin sahabbansa ba, idan kuma zai gaisa da mutum, Manzon Allah (s.a.w.a) ba ya janye hannunsa daga hannun mutumin har sai idan shi ne ya janye, saboda haka idan mutum ya gaisa da shi sai ya janye hannunsa daga nasa”.
c) – Nuna Rashin Amincewa Cikin Magana
Nuna rashin amincewa da katse mutum yayin da yake magana bai kamata ba. Kulayni, ta hanyar da aka sani, ya ruwaito Abi Abdillah al-Sadik (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Wanda ya katse dan’uwansa musulmi da ke magana a tsakiyar maganarsa tamkar ya kwarzane fuskarsa ne”.